Jump to content

Bankin Urwego

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bankin Urwego
Bayanai
Iri kamfani
Masana'anta financial services (en) Fassara
Aiki
Kayayyaki
loan (en) Fassara
Mulki
Hedkwata Kigali
Tarihi
Ƙirƙira 2007

urwegobank.com


Bankin Urwego (Urwego) karamin banki ne na kasar Rwanda wanda aka gina akan ka'idojin kiristanci. Kuma ya samu lasisi daga babban bankin kasar Rwanda wanda shine mai bada lasisi ga bankuna.

Kungiyar masu jin kan duniya sune suka kirkiro shi a 1997 a matsayin bankin yankin Urwego, ya shiga cibiyar Hope International a 2005. Sannan a 2007 yayi hadaka da bankin Opportunity International na Rwanda wanda ya zama bankin Urwego Opportunity. Wanda da anincewar babban bankin Rwanda, Opportunity International ta saida ma Hope International kashi hamsin na hannun jarinta na Urwego a 2017 wanda Hope International ta zama tana da kashi casa'in da tara na hannun jarin Urwego wanda kungiyar masu jin kan ta cigaba da rike kashi daya na hannun jarin.

A watan Yuli a shekarar 2019 Urwego nada rassa guda sha biyar, wanda bakwai daga cikinsu harda hedikwatar bankin suna a Kigali babban birnin kasar Rwanda.